A jihar New Jersey, mutane uku ne suka jikkata, a lokacin da suke tattaki na zanga-zangar wariyar launin fata da ke faruwa yanzu a haka a Amurka mai suna BLACK LIVES MATTER, a lokacin da barewa ta zabga da gudu ta abkawa masu gangami juma’ar da ta gabata.

A lokacin da jama’a suke tattakin ne akan titin Route 533, wata barewa daga cikin wata makarantar sakantar ta fito da gudu, kamar yadda bayanan ‘yan sanda suka bayar.

Wata mata mai shekaru 69 ta samu mummunan rauni, inda akai kaita babban asibitin yankin saboda ta samu buguwa a kanta.

Daga farko ana kula da ita ne a sashen ko-ta-kwana, amma daga bayan ‘yan sanda sun ce ta fara samun sauki.

Zanga-zangar ta samu hallartar mutane 1,000, inda suka rike da alamomi dake cewa “dukannin mu launin fatar mu daya” da “ku dena kashe mu”.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *