An karkare zaben dan kwamiti na wata mazaba a jihar Idaho dake Amurka ta jefa kwandala biyo bayan samun adadin kuri’u iri daya da ‘yan takarar suka yi.

A watan da ya gabata ne, ‘yan jam’iyyar Republican Carol R. Davey da Brock Fazier kowannen su ya samu kuri’u 36.

Dokar jihar Idaho tace idan aka yi kunnen doki a adadin kuri’u, to za’a yanke shawara ne ta jefa kwandala. Wannan doka dai an samar da ita ne tun shekara ta 1970.

Davey ya zabi kai biyo bayan dama da akawun mazabar ya bashi, amma bayan jefa, sai kwandalar ta nuna kafa, lamarin da ya baiwa Frazier nasara. An baiwa jama’a damar kallon jifan kwandala din, har suna daukar hotuna da bidiyoyi suna sakawa akan shafukan sada zumunta.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *