Kungiyar rajin kare hakkin bil adama na Amnesty International Larabannin ta saki gwamnatin tarayya saboda tsare Nastura da tayi, wanda ya shirya gangami akan kalubalen rashin tsaro da ya addabi mutanen Katsina.

Isa Sanusi, kakakin kungiyar, ya yi kiran gaggawa ga gwamnati akan ta sako Sharif wanda shine shugaban Kwamitin Amintattu na Gamayyar Kungiyoyin Arewa.

A wata sanarwa da ya fitar jiya, Darektan ayyuka na kungiyar Aminu Adam ya bayyana cewa ‘yan sanda sun tsare Sharif ne biyo bayan zanga-zangar lumana da ya shirya ranar Talata.

Ya kara da cewa bayan gangamin, Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Katsina ya gayyaci shugabannin kungiyar domin tattaunawa a ofishin sa.

Sanusi yace “dole gwamnatin Najeriya ta saki Nastura Ashir Sharif ba tare da bata lokaci ba, saboda babu abunda yayi illa bude bakin sa domin kare rayukan mutane da kuma kira a kawo karshen cabewar rashin tsaro a duk fadin arewacin Najeriya.

“Kira kawai yake musu akan su yi akin su”

“Tsare shi da aka yi, kamar wani yunkuri ne na razana shi da ragowar masu zanga-zangar lumana daga ‘yancin su na taruwa, da furta albarkacin bakin su.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *