Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Babagana Manguno ya jagoranci tawagar manyan hafsoshin tsaro zuwa jihar Katsina bayan zanga-zangar da aka gudanar a jihar ta nuna adawa matsalar tsaro a jihar.

Jim kadan bayan sun sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na Umaru Musa ‘Yar Aduwa dake Katsina, sun wuce kai tsaye zuwa gidan gwamnatin jihar inda suka shiga ganawar sirri da gwamna Aminu Bello Masari, da wasu mukarraban gwamnatinsa.

Daga cikin tawagar akwai shugaban hukumar jami’an tsaron farin kaya DSS, Yusuf Magaji Bichi, babban sufeton ‘yan sanda Muhammad Adamu, da sauransu.

Masu zanga-zangar dai sun bukaci gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, da gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari su gaggauta kawo karshen matsalar tsaro a jihar.

Sai dai wasu rahotanni sun tabbatar da cewa jami’an ‘yan sanda sun kama tare da tsare shugaban masu zanga-zangar Nastura Ashir Sharif sakamakon zanga-zangar da ya shirya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *