Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa hukumar yaki da cin hanci ta jihar zata cigaba da binciken tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II da zargin almundahana.

Gwamnan ya bayyana hakan ne Litinin dinnan a lokacin da yake ganawa da manema labarai da ya gudana a dakin taron Africa House dake gidan gwamnatin Kano.

Gwamnan yana amsa tambaya ne akan batutuwan shari’a dake zagaye da samar da masarautu da kuma garambawul din da ya yi wa masarautu.

“Eh akan abubuwa masu nasaba da shari’a, wadanda suka tsagaita hanzarin gudanar da garambawul din, amma cewa yanzu babu wannan tsohon Sarkin, kotu ta yanke shawarar watsi da wadannan kararrakin, kuma hukumar yaki da cin hanci zata iya binciken tsohon sarkin kamar yadda doka ta tanadar” a cewar Ganduje.

Gandujen ya kara da cewa Kungiyar Dattawan Kano ita ma baza ta iya dakatar da garambawul din ba, tunda kotu ta yi kafar ungulu da karar da ta shigar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *