Wata gyatuma mai shekara 65 a kasar Indonesiya ta auri yaron da ta rena mai shekara 24 bayan da ya nemi auren ta.
Mbah Gambreng and Ardi Waras | Image: CEN/Australscope

Rahotanni na nuna Mbah Gambreng wadda ta dauki Ardi Waras a shekarar da ta gabata domin ta ringa kula da shi ta aure shi a garin Sumatra ta Kudu dake kasar Indonisiya.

Ma’auratan biyu na zama tare ne, a cewar tsohuwar, kuma bata taba tunanin auren auren yaron bayan daukar nauyin shi.

Gambreng ta gaya wa manema labarai cewa kawai ce wa saurayin tayi “yayi maza maza yayi aure” biyo bayan aurar da ‘ya’yan ta mata su uku wadanda suma ta dauko su domin kula da su.

“Nayi mamaki a lokacin da yace ni yake so ya aura” a cewar matar.

Waras ya biya kudin sadakin ta na 100,000 IDR (Nera 2,742) wanda ta amince da shi. Hotunan bikin ya nuna ma’auratan suna murmushi, da rike hannu da rungumar juna.

A auren addinin Musulunci da ake yi a Indonesiya, miji ne ko mahaifin sa yake biyan kudin aure da kayan gida a lokacin da ake aure a matsayin sadaki.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *