A ranar Litinin dinnan ne, jama’ar jihar Katsina suka kalubalanci gwamantin tarayya, a kan ta bayyana sunayen shugabanin gargajiya da aka ce suna taimaka wa ‘yan ta’adda a jihar.

Sun bayyana cewa idan ba a yi hakan ba, to kowa zai dora wa kowa laifi, saboda haka gwamma gwamnatin Tarayya ta fito ta bayyana sunayen shugabanin gargajiya da kama su, da gurfanar da su a gaban alkali idan har suna da hannu a rashin tsaro da yanzu ya addabi jihar, lamarin da ya yi dalilin daruruwan rayuka.

Shugabannin al-ummomin da aka fi kai wa hari sun bayyana wa manema labarai cewa dole ne a fitar da sunayen masu hannu wajen taimaka wa ta’addanci domin maganin zarge-zarge.

Wannan kiraye-kiraye ya biyo bayan tonon asiri da babban mai taimaka wa shugaban kasa akan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya yi, inda ya bayyana cewa akwai shugabannin gargajiya da ke taimaka wa ‘yan bindiga wajen tserewa a duk lokacin da jami’an tsaro suka je kai musu hari.

Ya kara da cewa “ba wai muna zargin su ba ne kai tsaye, amma da gaske akwai shugabanin gargajiya a jihar Katsina da aka samu da hannu wajen hada kai da ‘yan bindiga domin zaluntar mutanensu. “A jihar Zamfara da ke makwabtaka, akwai sarakuna da hakimai wadanda duk sun rasa kujerunsu. Abun da yake faruwa shi ne akwai yake amfana daga irin wannan rubuwa na al-umma.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *