Amanda Bennett ta rattaba murabus daga kan kujerar matsayinta na Shugabar Muryar Amurka, mako daya da fara aikin Michael Pack da Donald Trump ya kawo don jan ragamar ma’aikatar yada labaran Amurka ta United State Agency for Global Media.

Amanda tsohuwar ‘yar jarida ce, kuma ta fara shugabantar Muryar Amurka ne a shekarar 2016 zuwa wannan lokaci da ta yi murabus a watan nan na Yunin shekarar 2020. Sannan ba ita kadai ta yi murabus ba, don kuwa har ma da mataimakiyarta mai suna Sandra Sugawara wacce ita ma ‘yar jaridar ce.

Duk da cewa ana jinjina wa Amanda game da yadda ta fadada ayyukan Muryar Amurka ta bangare daban-daban cikin harsuna 47 da ke isar da labarai da rahotanni ta hanyar radiyo da talbijin da ma yanar gizo ga kasashen duniya, amma kuma wasu na kallon tana da rauni a shugabancin da ta yi.

Musamman yadda a ka dinga samun ragabza iri-iri masu alaka da almundahana a kololuwar gidan da kuma yadda ta fuskanci matsalolin wasu laifuffuka da suka taso daga wasu sashen harsunan Muryar Amurka kamar Sashen harshen Mandarin na Sinawa da kuma Sashen Hausa.

Wanda wasu ke gani ta dauki zafafan hukunci don kare kujerarta da kuma kokarin binne gira-gizan laifuffukan da a ke tafkawa a shugabancinta da suka dame tare da shanye matsalar dakile tattaunawar sashen Mandarin da kuma karbar kyautar da ‘yan Sashen Hausa suka yi.

Laifuffukan da a ganin wasu kwararru, matakan ladabtar wa ya kamata a dauka ga ma’aikatan ba matakin kora ba. Wanda wasu ma’aikatan sun shafe sama da shekaru 30 suna aiki a gidan ba tare da yin laifi ko daya ba.

Ko ma dai mene ne, masu kallon al’amura na ganin tafiyar Amanda na da nasaba da sabon shugaban da a ka kawo ma’aikatar wanda ko shakka babu za a yi abin nan ne da Bahaushe ke cewa, Sarki goma zamani goma.

Micheal Pack ne sabon shugaban hukumar yada labaran Amurkar ta ’USAGM’ a takaice wacce Muryar Amurka ke karkashin jagorancinta, mutum ne kwararren mai shirya fina-finan kundin-gaskiya ko tarihi, kuma dan jam’iyyar ’Republican’ ne yana kuma da ra’ayin ‘yan mazan jiya.

Sannan kamar yadda Amanda ta ce a sanarwa murabus dinta, sabon shugaban na da ikon ya zabi duk wanda ya ke bukata don nadawa a kujerar da ta yi ban-kwana da ita ko da dadi ko babu.

Haka zalika ana sa ran zai kawo kyakkyawan canji a hukumar da a ka kafa don kare martabar Amurka a idon duniya a ke kuma daukar nauyinta da dukiyar harajin Amurkawa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *