Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce jami’an sojin Najeriya na aiki ba dare ba rana wajen yaki da ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso yammacin Najeriya.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ta samu sanya hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a Garba Shehu.

Shugaban ya ce zanga-zangar da ake yi don nuna adawa da kashe-kashen da ke faruwa a arewacin Najeriya na iya ɓata ayyukan da jami’an sojin ke yi a yankin.

Ya bukaci al’ummomin jihar Katsina da kada su fidda tsammani kan sojoji da suka dau shekaru da dama suna shawo kan rikice-rikice, da Najeriya ta tsinci kanta a ciki.

Sanarwar ta kuma ba ‘yan Najeriya tabbacin cewa dakarun sojin za su iya magance matsalar fashi da makami da sauransu, tare da yin kida da a kara hakuri.

Wannan na zuwa ne bayan zanga-zangar da wasu kungiyoyi da dama suka gudanar a birnin Katsina.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *