MUHAMMADU BUHARI
SHUGABAN NAJERIYA

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai halarci taron ka kasar China za ta yi da wasu kasashen Afrika ta hanyar amfani da fasahar zamani a wani mataki na yaki da cutar korona.

Za a fara taron ne da misalin karfe 12 da miti 50 na ranar Laraban nan karkashin jagorancin shugaban kasar China Xi Jinping, wanda zai gabatar da jawabai a farkon taron.

Shugabannin kasashen Afrika, da suka hada da majalisar kungiyar tarayyar Afrika da kuma shugaban kungiyar dake mulkin karba-karba neza su halarci taron.

Har ila yau ana sa ran sakataran majalisar dinkin duniya da daraktan hukumar lafiya ta duniya ne za su yi jawabi na musamman.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *