Biyo bayan hare-haren da 'yan bindiga suke cigaba da kaiwa kauyukan Katsina da Zamfara da Sakkwato, ta kasa shawo kan lamarin, jama'ar garin Kadisau da aka kai wa hari a makon da ya gabata sun yi korafi akan nuna rashin kula da gwamnatin Aminu Bello Masari take musu yayin da mata da marayu suke zaune a cikin makarantu tare da rashin abinci da tufafi. To tambayar a nan itace ko akwai hannun gwamnati a wadannan hare-hare? Radiyon Talaka ya nemi jin ta bakin gwamnatin Jihar Katsina da ta Jiha amma har ya zuwa yanzu babu martani, shi yasa ta yi hira da dan garin Kadisau mai suna Bashir Mamman Dan Inna. A saurari cikakkiyar hirar a sautin dake saman shafi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *