YEMI OSINBAJO
MATAIMAKIN SHUGABAN NAJERIYA

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, ya ce bai bukaci a dakatar da shirin yiwa kasa hidima da dalibai ke yi a karshen karatunsu ba.

Mai taimakawa mataimakin shugaban kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a Laolu Akande ne ya bayyana haka a shafinsa na twitter.

Ya furta hakan ne biyo bayan wasu rahotanni na yanar gizo da ke cewa kwamitin farfado da tattalin arzikin kasa da mataimakin shugaban kasan ke jagoranta ya bukaci a dakatar da tsarin na NYSC zuwa shekaru biyu masu zuwa.

Ya ce abin da kwamitin ya bada shawara akai shine ba daliban damar wucewa kai tsaye wuraren da aka turasu gudanar da bautar kasa ba tare da sun yi zamar sansanin yiwa kasa hidiman ba.

Ya ce shawarar ta biyo bayan kokarin da hukumomin lafiya ke yi na dakile yaduwar cutar korona, musamman ma kaucewa taron jama’a.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *