Ministar kula da harkokin mata da ci gaban kasa Pauline Tallen, ta ba ‘yan Najeriya tabbacin cewa gwamnatin tarayya za ta yi dukkanin mai yiwuwa wajen magance matsalar fyade a fadin kasar nan.

Tallen ta bada wannan tabbacin ne a lokacin da tawagar kungiyar mata matasa suka kai mata ziyara a oafishin ta dake Abuja, a wani bangare na gangamin yaki da fyade.

Ministar ta bayyana fyade a matsayin babbar barazana ta bukaci ‘yan Najeriya su hada hannu wajen yaki da annobar tare da tabbatar da nasara ta samu.

Ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a kaddamar da wani gangami na musamman da zai wayar da kan mutane kan hanyoyin da za su iya bada gudunmawa wajen magance matsalar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *