Wasu da a ke kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun yi awon gaba da shugaban karamar hukumar Shelleng da ke jihar Adamawa mai suna Mista Kama Lazarus Bakta

An dai sace wannan jami’in ne tsakar daren ranar Talatar 16 ga watan Yunin shekarar nan ta 2020 a garin Bakta inda nan ne garinsa.

Ya zuwa yanzu dai ba a san me masu garkuwar da suka sace shi suke so ba. Sannan mun yi kokarin jin ta bakin jami’an tsaro kan lamarin amma ya zuwa yanzu ba mu sami nasarar samun kowa ba.

Amma wakilinmu na Adamawa zai ci gaba da bi mana labarin don jin yadda za ta kaya tsakanin barayin mutanen da kuma shi mataimakin shugaban karamar hukumar ta shelleng a jihar Adamawa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *