Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin shuka bishiyoyi miliyan 26 a yankin Arewacin Najeriya.

Shugaban ya ba da umarnin ne ga hukumar da ke kula da shuka itatuwa a yankunan da ke da barazanar kwararowar hamada.

Za a shuka bishiyoyin ne a jihohi takwas da suka haɗa da Borno da Jigawa da Katsina da Sokoto da Yobe da Kebbi da Kano da kuma Zamfara.

Ya ce wannan na daga cikin alkawuran da ya ɗauka na shuka bishiyoyin a yayin taron Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 74.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *