Shugaban kungiyar likitocin ta Najeriya reshen jihar Adamawa Dokta Tonde Gargah ya ce likitoci dari 3 ne kacal ke kula da mutane miliyan hudu a jihar Adamawa.

Shugaban kungiyar ya bayyana hakan ne a ganawar da aka yi ranar Juma’a a Yola.

Yawan likitocin ya gaza wanda Kungiyar Lafiya ta Duniya suka ba da.

A yanzu haka ko wani Likita daya a jihar za’a iya cewa yana kula da akalla mutane 13,300.

Ya kara da cewa wannan ba karamin aiki bane.

Shugaban ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta duba lafiyar jiga-jigan likitocin don inganta jin dadinsu don samar da ingantaccen kiwon lafiya.

Gargah ya ce ana ci gaba da samun yawan al’umma musamman a karamar hukumar Yola ta Kudu.

Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta gina karin asibitoci don bunkasa lafiya.

Da yake mayar da martani, gwamnan jihar Ahmadu Fintiri ya ce, a cikin shekara guda gwamnatinsa ta sami gagarumin ci gaba da inganta rayuwar dan Adam a duk fadin jihar.

Fintiri ya ce bayan daukar sabbin malamai 2,000, gwamnati na shirin daukar sabbin ma’aikatan lafiya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *