Gwamnatin jahar Yobe ta kudiri aniyar wadatar da Jahar da Ruwan Sha ta hanyar samar da Sabbin  rijiyoyin burtsatse da kuma  tuka-tuka a fadin jahar.

Ma’aikatar samar da ruwa a jahar ta bayyana haka.

Ma’aikatar samar da ruwa ta ce za ta gyara kimanin rijiyoyin burtsatsen 50.

Ta ce an  samar da kayan aikin gyaran wanda suka lalace da kuma cire wasu dan sauya musu guri da ya dace.

Ma’aikatar ta ce aikin zai fara gudana a wasu kananan hukumomi na jahar da suka hada da Buni-Yadi, Buni-Gari, Damaturu da kuma Potiskum.

Aikin yana gudana ne karkashin jagorancin shugaban ma’aikatar Mohammed Malam Bukar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *