An kashe mutane 60 a wasu tagwayen hare-hare da ‘yan ta’addan da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne suka kai a jihar Borno.

Mazauna yankin sun ce ‘yan bindiga masu ɗauke da muggan makamai ciki har da na roka suka shiga garin Monguno.

Hare-haren da aka kai a Monguno da Nganzai na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan ‘yan ta’addan sun kashe a kalla mutane 81 a ƙauyen Gubio.

Tuni dai Kungiyar ISWAP dake ayyukan ta’addanci a ƙasashen yammacin Afirka ta bayyana cewa ita ta kai wadannan hare-hare.

Wani shaidan gani da ido a garin Monguno ya ce mayaƙan sun ƙona matattarar hukumomin bayar da agaji na Majalisar Dinkin Duniya tare da wani ofishin ‘yan sanda.

Ya ce ɗaruruwan farar hula ne aka raunata inda kuma asibitin garin ya cika har ake tilasta wa wasu masu raunuka da su tsaya a waje.

Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da kai wannan harin a wata sanarwa da ta fitar.
 

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *