ROTIMI AMAECHI
MINISTAN SUFURI

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da fitar da naira biliyan dari da 23 daga cikin kudaden da gwamnatin tarayya ta samu bashi daga kasar China domin aikin hanyar jirgin kasa na zamani daga Ibadan zuwa Kano.

Ministan sufuri Rotimi Amaechi ya bayyana haka, ya ce aikin wani bangare ne na aikin hanyar jirgin na jihohin Legas zuwa Kano, kuma za a fara aikin ne a watan Augusta.

Ya ce kasar China ne ta dauki nauyin samar da kudaden da wani kamfanin kasar zai gudanar a Najeriya.

A cewarsa majalisar zartaswa ta tarayya ta amince da bude wani asusu na musamman da za a rika tara kudade daga surufin jiragen kasan domin biyan gwamnatin kasar ta China.

Ya kara da cewa sufurin jiragen kasa daga Kaduna zuwa Abuja da aka fara jigilar fasinjoji dubu 3 yanzu ya koma dubu 4, sakamakon kara inganta harkokin.

Ya ce a baya lokacin da aka fara sufurin jiragen kasan gwamnatin tarayya na asarar naira milliyan 46 ko wane wata, amma yanzu tana samun ribar naira milliyan dari da 9 zuwa da 10 ko wanne wata.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *