Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta ce tsawa ta kashe wasu da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne a jamhuriyar Kamaru dake da makwabtaka da jihar.

Bayanin hakan na cikin sanarwar da mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Suleiman Nguroji ya fitar a Yola.

Rundunar na maida martani ne kan rahotanni da ake yadawa a shafukkan sada zumunta na cewa tsawar ta kashe mutanen ne a karamar hukumar Toungo dake jihar.

Nguroje ya ce ba a Najeriya aka samu mutuwar ‘yan ta’addan ba, sun mutu ne a kauyen Pawati dake kasar Kamaru.

Ra’ayi 1

Your email address will not be published. Required fields are marked *