Hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta ce an samu sabbin masu dauke da cutar korona 627 a Najeriya daga gwaje-gwajen da aka gudanar a cikin awa 24.

Hukumar ta bayyana hakan ne a shafin ta na twitter, inda ta ce yawan masu dauke da cutar a Najeriya yanzu ya kai dubu 15 da dari da 81.

A bayanan da ta wallafa a shafin jihar Legas ke da adadi mafi yawa na wadanda suka kamu da cutar da mutane 229, sai babban biirnin tarayya Abuja dake da mutane 65, jihar Abia an samu mutane 54.

Jihar Borno na da mutamne 42 da suka kamu, sai Oyo mai mutane 35, Rivers da Edo kowannen sun a da mutane 28, sai Gombe 27, Ogun 21, Plateau da Delta nada mutane 18 kowannen.

Sauran sun hada da jihar Bauchi da Kaduna dake da mutane goma-goma, Benue nada mutane 9 da suka kamu da cutar, sai Ondo 8, Kwara 6, Nasarawa da Enugu hur-hudu, sai Sokoto da Neja da kuma Kebbi masu mutum uku-uku, sannan Yobe da Kano nada mutum dai-dai.

Baya ga wadanda suka kamu da cutar, ta ce adadin wadanda suka warke yanzu ya kai dubu 4 da 891.

Sai kuma mutane 399 da suka mutu sakamakon kamuwa da cutar a fadin Najeriya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *