IBRAHIM MAGU
SHUGABAN EFCC


Shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC Ibrahim Magu, ya ce hukumar ba ta da hannu a kama Ramon Abbas da aka fi sani da Hushpuppi.
Magu wanda ya bayyana haka a lokacin da ake zantawa dashi a wata kafar talabijin, ya ce har yanzu hukumar ba ta shiga cikin batun wanda aka kaman ba.
Ya ce aikin hukumar ta EFCC ba kamawa da gurfanar da masu aikata laifin damfara bane, domin tana saisaita rayuwar masu aikata laifukka makamantan haka da suka nemi tuba.
Rahotanni sun tabbatar da cewa hukumar ‘yan sanda ta Interpol da hukumar leken asiri ta FBI sun kama Hashpuppi da abokinsa ne a hadaddiyar daular Larabawa Dubai.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *