Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta gargadi al’ummomin kananan hukumomin Kauru da Zangon Kataf kan saba dokar hana fita ta tsawon awa 24 da gwamnatin jihar Kaduna ta sa a yankin.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar Mohammed Jalige ya fitar, ta ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna Umar Muri ya bada gargadin cewa duk wanda aka samu yana saba dokar zai yabawa aya zakin ta.

Muri ya ce duk da cewa jami’an tsaro sun kwantar da tarzomar, gwamnatin jihar ta fadada dokar hana fitar ta tsawon awa 24 zuwa dukkanin sauran sassan kananan hukumomin 2.

Ya ce an dauki matakin ne domin dakile duk wata fargaba na sake barkewar rikicin a nan gaba.

Rundunar ‘yan sandan ta kuma bukaci al’umma su rungumi zaman lafiya da fahimtar juna musamman a wannan lokaci da damina da harkokin noma ke ci gaba da kankama.

Gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fitar ce biyo bayan hatsaniya da aka samu a masarautar Atyap da Chawai a kananan hukumomin 2 sakamakon rikici kan gona.  

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *