Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana bangaren wasanni a matsayin hanyar samar da zaman lafiya da ci gaban kasa.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da dandalin wasanni da aka sanyawa sunan marigayi Moshood Abiola, a wani bangare na murnar zagayowar ranar dimokradiyya.

Shugaban wanda ya samu wakilcin ministan babban birnin tarayya Abuja, Muhammad Bello, ya bayyana muhimmanci da yake akwai na kara inganta harkokin wasanni ta yadda zai yi gogayya da na kasashen da suka ci gaba.

Ya ce gwamnatin tarayya za ta ci gaba da maida hankali tare da inganta harkokin wasanni, domin a cewarsa ba wata gwamnatin da ta san abin da take da za ta yi watsi da bangaren.

A nasa jawabin ministan kula da harkokin matasa da wasanni Sunday Dare, ya godewa shugaban  kasa Muhammadu Buhari na amincewa da canzawa filin wasan suna.

Ya kara da cewa akwai shirye-shirye da ake na kara inganta filin wasan ta yadda zai zama daya daga cikin wadanda suke sahun gaba a Najeriya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *