Biyo bayan jawabin da yayi wanda aka yada a kafofin yada labarai Juma’ar nan akan bikin ranar Dimukradiyya, Shugaba Buhari ya bar baya da kura saboda jama’a sun nuna rashin gamsuwarsu da jawabin sa, inda suke gani kamar bai fahimci matsaloli dake addabar jama’a ba, kuma sun kara da cewa babu wani cigaba ma a mulkin dimukradiyyan baki dayan ta.

A jawabin sa, shugaban ya dauki tsawon lokaci yana bayani akan cigaban da gwamnatin say a kawo dangane da rashin ayyukan yi, tattalin arziki, annobar Korona da dimukraddiya, bangaren noma, da saukin gudanar da kasuwanci, da makamashi, da harkokin safara, da ilimi, da na’urorin zamani, samar da muhallin zama da ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga, da bin doka da oda ya yaki da cin hanci da rashawa, da matasa, mata da gajiyayyu.

Amma da Radiyon Talaka ya tuntubi jama’a domin jin ra’ayoyinsu akan bikin dimukradiyyan da kuma irin cigaban da aka samu, martanin da suka bayar ya sha ban-ban da na shugaban.

Aishatu Bint Shafi’i daga jihar Kaduna cewa tayi “Mu yau ba mu maganar demokaraɗiyyar ma, kashe mana yan uwa da ake kaɗai ya ishe mu shedar bata kare mu talakawa da komai ba sai takaici”

“Ci gaban mai hak’ar rijiya: an kashe talaka, an yi wa matansa da ‘ya’yansa fya’de, an wulak’anta shi, an talauta shi, an dawwamar da shi cikin jahilci.” Inji Bashir Yahuza Malumfashi dan jarida daga jihar Katsina amma yana zama Abuja.

Matashi kuma dan jami’ar Ahmadu Bello mai suna Musa Musa D ya nuna rashin gamsuwar shi “Har yanzu nazarin da na ke yi kenan. Sannan na fahimci cewa idon mutane ya bude da sata, cin mutuncin juna, rashin kishi, hassada, bangar siyasa da munafunci.

Ta yadda duk mu ka kalli siyasa a dimukuradiyya za mu ga cewa sharri da rashin jin dadin ya fi jin dadin yawa. Ana sata ana kuma kashe mu, an maishe mu bayi. Ba ka ma isa ka fadi gaskiya ba sai an kama ka.Tir da wannan dabia’ar siyasa”.

A wadannan shekarun da suka gabata, jama’a suna kara kukan rashin tsaro, rashin ayyukan yi, talauci da rashin ababen more rayuwa daga gwamnatin Buhari, alhali kuwa, gwamnatin tana cigaba da jaddada cewa tana kawo cigaba a wadannan bangarorin, da ma wasu bangarorin baki daya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *