Duk irin kuwwa da karaji da muke yi kan abubuwan da ake yi na aikin ta'addanci da miyagun mutane suke yi a Katsina da Sokoto da Zamfara da Birnin-Gwari, alamu sun nuna cewar Abuja bata san muna yi ba.

Duk da irin yadda kafafen yada labarai suka dinga bada labarin zubar da jinin bayin Allah da ake yi, amma Abuja ba ta sani ba, ko kuma Abuja bata da damuwa kan abubuwan da suke faruwa.

Shugaban kasa har yayi jawabinsa na karfe bakwai na safiyar sha-biyu ga watan Yunin shekarar nan ta 2020 ya gama a yau din nan ranar dimukuradiyya, babu inda ya nuna ya san wani abu wai shi zubda jini na faruwa a Katsina bare kuma Sokoto ko Zamfara bare kuma irin su Borno.

Da alamun wadanda ke da hakkin sanar da Abuja halin da ake ciki a kasa baki daya, basa yin aikinsu. Ko irin shirun minti daya Abuja bata yi ba don nuna jimami kan kashe-kashen da ke aukuwa.

Don haka, ya rage namu, mu al’ummar da ake zalinta, mu sani cewar ci gabanmu baya Abuja, Gwamnatin tsakiya dake Abuja ba tada wani tashin hankali akan Abinda bai shafi Abuja ba.

Allah muke roko yaji kukanmu, ya yaye mana wadannan masifu da muke fama da su. Shugabanninmu kuma amana ce suka dauka, idan sunyi Abinda ya dace kansu, idan sun cigaba da kauda kai rayuka da dukiyoyin suna salwanta, su sani alkawarin Allah gaskiya ne kuma abin tambaya. Wanda ya yi nagari kansa!

Yasir Ramadan Gwale
12-06-2020

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *