Gwamnatin tarayya ta ce an dawo da mutane 102 Najeriya daga kasar Masar.

Ministan harkokin kasashen ketare Geoffrey Onyeama ya tabbatar da hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Ya ce ana dakon isowar wasu karin mutane 260 daga ƙasar Indiya a ranar Asabar dinnan.

A cewarsa, jirgin Egypt Air ne ya dawo da mutanen, sannan ana sa ran jirgin Air Peace zai dawo da na Indiya.

A baya dai Najeriya ta dawo da mutanen ta dake zaune a wasu kasashen duniya sakamakon bullar cutar korona, inda ake killace duk wanda ya dawo na tsawon kwanaki 14 kamar yadda masana harkokin lafiya suka shawarta.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *