A garin Richmond dake Jihar South Carolina dake Amurka, jami’an tsaro na neman taimakon jama’a wajen neman wani miji da mata wadanda hotunan bidiyo ya nuna su suna amfani da bindiga wajen gudanar da fashi da makamin kwalbar lemon Pepsi mai girman lita biyu a wani shagon Pizza Hut.

Mai kula da shagon, ya bayyana cewa wani miji da mata wadanda ba a san su ba sun tunkare shi inda suka ce abincin da suka saya domin a tura musu gida bai zo da robar lemon pepsi din da suka saya ba.

An zargin mutumin da fito da bindiga da nuna wa manajan shagon inda matar da dauki robar lemo mai girman lita biyu daga bayan kanta, sannan suka yi gaba.

Hukumar ‘yan sanda ta Richland ta fitar da hotunan mutanen da ake zargi inda ya saka akan shafin ta na twitter, kuma ‘yan sandan sun nemi a kira wata lambar waya a bayyana idan aka gan su.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *