Ministan kula da harkokin sufuri Rotimi Amaechi, ya ce kasar China na taimakawa Najeriya ta bangarori da dama.

Amaechi ya bayyana hakan ne a wani bayani da ya yiwa manema labarai a sakon zagayowar ranar dimokradiyya.

Ya kara da cewa kasar ta China tun a baya ta dade tana kokarin ganin ci gaban Najeriya musamman ma yanzu da ta amince da fitar da wasu kudade ga gwamnatin tarayya da za a yi amfani dasu wajen samar da ababen more rayuwa.

Amaechi ya ce a baya Kasar ta Sin ta fitar da dala billiyan daya da milliyan dari 6 domin aikin titin jirgin kasa na Lagos zuwa Ibadan, kuma nan da watan Oktoba mai zuwa ana sa ran za ta turowa Najeriya dala billiyan 5 da milliyan dari 3.

Ya ce ana ci gaba da aikin layin dogo na zamani da zai taso daga Legas zuwa Kano, inda zai bi ta kan iyakar Nijar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *