Shugaban Kwamitin da shugaban kasa ya nada domin yaki da annobar cutar Korona, Sani Aliyu, a sanarwa da ya fitar a birnin Abuja Alhamis dinnan, ya bayyana cewa hukumomin safarar jiragen sama da cikin gida, sune suke da alhakin samar da lokacin da jiragen sama na cikin gida zasu dawo aiki dangane da shirin su.

A watan Maris din wannan shekara ne gwamnatin Tarayya ta rufe harkar zirga zirga na jiragen sama domin rage yaduwar cutar Korona.

Aliyu na kara da cewa Kwamitin sa na gab da samun karin bayanai daga ma’aikatun harkar jiragen sama akan irin da suka yi.

Yace ba’a ce ranar 21 za’a bude ba, an dai baiwa hukumomin jiragen sama makonni uku su shirya, kuma har yanzu shiryawa suke. Yace har yanzu basu tambayi halin da ake ciki amma suna jiran a basu karin bayani.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *