AKIN ABAYOMI
KWAMISHINAN LAFIYA NA LEGAS

Gwamnatin jihar Legas ta ce mutane 90 da suka kamu da cutar korona a jihar sun warke daga cutar, kuma an sallame su.

Ma’aikatar lafiya ta jihar ta tabbatar da haka ga manema labarai.

Ta ce gwaje-gwajen da aka yi na baya-bayan nan guda 2 ga mutanen sun nuna cewa basa dauke da cutar.

Ma’aikatar ta ce daga cikin mutanen da suka warke akwai 30 mata da kuma maza guda 60, wanda tuni aka amince su ci gaba da huldar su ta yau da kullum da al’umma.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *