MUHAMMAD BABANDEDE

Hukumar kula da masu shige da fice ta Najeriya ta ce tana hada hannu da hukumar bunkasa harkokin noma NALDA ta kasa domin samar da wadataccen abinci.

Shugaban hukumar Muhammad Babandede ya bayyana haka a lokacin da ya amshi bakuncin tawagar hukumar ta NALDA a shelkwatarta dake Abuja.

A cikin wata sanarwa da ta fito ta hannun mai magana da yawun hukumar Sunday James, ya ce tsarin da za su fito dashi zai yi aiki a dukkanin kananan hukumomin Najeriya 774.

Babandede ya ce hukumar da yake jagoranta na da muhimmiyar rawa da za ta iya takawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasa, tare da nunawa jami’an ta muhimmancin noma.

A nasa jawabin shugaban hukumar bunkasa harkokin noman Paul Ikonne, ya ce ziyarar ta su ta na da matukar muhimmanci, kuma umurni ne na shugaban kasa Muhammadu Buhari kan bin hanyoyin da suka kamata wajen samar da wadataccen abinci a Najeriya.

Ya ce hukumarsa ta fito da shiri na musamman mai taken “mu koma gona”, wanda zai wayar da kan ‘yan kasa kan muhimancin rungumar harkokin noma.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *