ALI NDUME

Dan majakisar dattawa mai wakiltar mazabar jihar Borno ta yamma, Ali Ndume, ya ce akwai bukatar a mayar da aiyukan dukkan majalisun tarayya na wucin gadi.

Ndume ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a Abuja.

Ya ce yin hakan zai taimaka wajen rage albashin da ake kashewa wajen biyan albashin ‘yan majalisar da kudin tafiyar da harkokin gwamnatin kasa.

Ndume ya ce ya kamata a kuma rage albashin manyan ma’aikatan gwamnatin tarayya domin samun kudin da za a yi manyan aiyukan raya kasa.

Dan majalisar ya kara da cewa bai kamata a ci gaba da tafiya a tsarin kashe kaso 70 na kasafin kudi a kan tafiyar da aikin gwamnati da ma’aikata ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *