Mai shari’a Monica Bolna’an Dongban-Mensem ta zama shugabar Kotun Daukaka Kara ta Najeriya bayan amincewar da Majalisa ta yi na zabin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika musu.

Monica Bolna’an Dongban-Mensem, Shugabar Kotun Daukaka Kara
Hoto: justicemenseng,com

Monica dai ‘yar asalin jihar Filato ce kuma kwararriya a harka shari’a. Ta yi digirinta na daya dana biyu a fannin shari’a daga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria a jihar Kadunar Najeriya.

Daga baya ta yi wata babbar diflomar a Cibiyar Koyon Ilmi Shari’a Mai Zurfi da ke Jami’ar London. Ta yi ayyuka da dama a fannin abin da ta kware na tsawon shekaru. Sannan ta na daga cikin masu neman daidaiton yara da mata a cikin al’umma.

Mai Shari’a Monica a daya daga halartar wasannin bunkasa matasa
Hoto: justicemenseng,com

Ana sa ran nadin nata zai kawo kyakkyawar gudunmawa a fannin shari’un da ke da nasaba da daukaka kara da kuma yanke hukunce-hukunce cikin gaskiya da adalci.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *