NASIR AHMAD EL-RUFAI

Gwamnatin jihar Kaduna, ta sanya dokar hana fita a wasu yankuna biyu na jihar sakamakon rikicin kabilanci da ya barke a tsakanin Hausawa da wasu kabilun kudancin jihar kan filin noma.

Wata sanarwar da ta fito daga gwamnatin jihar, ta ce dokar ta tsawon sa’o’i 24, ta shafi Masarautun Atiyep da ke karamar hukumar Zangon Kataf da kuma Chawai ta karamar hukumar Kaura.

Rikicin dai ya sa wasu matasa datse hanyoyin mota inda suke barazana ga matafiya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *