BABAGANA ZULUM
GWAMNAN BORNO

Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum, ya tabbatar da mutuwar mutane 81 a wani sabon hari da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kai.

Daya daga cikin wadanda suka ga yadda ‘yan Boko Haram suka halaka jama’a a kauyen Faduma Kolomdi da ke karamar hukumar Gubio ta jihar Borno a ranar Talata, ya bada labarin yadda aka yaudaresu.

A lokacin da wani shaidan gani da ido yake tattaunawa Gwamnan a lokacin danya ziyarci kauyen, ya ce an kashe mutanen ne tare da illata wasu 13 da kuma yin garkuwa da wasu bakwai.

Ya kara da cewa ‘yan ta’addan sun isa garin ne a motocin yaki wurin karfe 10 na safe.

Shima Gwamna Zulum ya yi kira ga rundunar soji da su kara kokari wajen yaki da ‘yan ta’addan.

Gwamnan ya kwatanta harin da mummunan al’amari kuma abun takaici da alhini.

Gwamnan ya kwashe mutum biyar da suka samu raunuka inda ya mika su asibiti da kansa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *