Rundunar ‘yan sanda a Kano, ta tsare wani mutum mai shekara 32, Muhammad Alfa, wanda ake zargi da yi wa mata sama da 40 fyade a shekarar da ta gabata.

Kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna ya tabbatar da hakan a sanarwa da ya yi Laraban nan a Kano.

Haruna ya bayyana cewa an kama mutumin da ake zargi ranar 10 ga watan Yuni misalin karfe 2 na dare, a lokacin da ya tsallaka ya shiga wani gida a garin Kwanar Dangora dake Kano da nufin yin fyade.

Ya kara da cewa, mutumin wanda aka fi sani da “Mai Siket” ya dade yana shiga gidajen mutane domin samun fahimtar wadanda zai afka wa na tsawon lokaci, har ta kai ga wasu daga cikinsu suna kiran shi “mugun aljani”.

“Mutumin da ake zargi ya tsallaka zuwa wani gida a garin Kwanar Dangora, inda ya shiga dakin yara, to hakan ya saka mahaifiyar yaran ta kama, sannan ta sanar wa makota.

“Sai mutumin ya yi kokarin tserewa amma makota suka kama shi, sannan suka mika shi ga ‘yan sanda,” a cewar Kakakin.

Haruna ya bayyana cewa a binciken da suka yi, wanda ake zargi ya amince akan cewa ya yi wa mata sama da 40 fyade a shekara daya da ta gabata, inda yace wasu daga cikin matan akwai yara da wata tsohuwa mai shekara 80.

Ya kara da cewa ofishinsu ya fara samun korafe- korafe daga wasu daga cikin matan da ya yi wa fyade da iyalansu.

Kakakin ya ce Kwamishinan ‘Yan Sanda, Mr Habu Ahmad ya ba da umarnin a kai mutumin da ake zargi zuwa Hukumar Binciken Laifuka wato CID na jiha domin a cigaba da yin bincike.

Kamar yadda ya ce, za a gurfanar da wanda ake zargi a gaban alkali bayan kammala bincike.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *