Rahotanni na nuna cewa mayakan sa kai na Boko Haram sun kashe a kalla mutane 70 a kauyen Foduma Koromaiya dake misalin kilomita 11 daga garin Gazaure dake kamar hukumar Gubio a Jihar Borno Talatannan.

Gubio dai ta kasance misalin kilomita 96 daga garin Maiduguri dake arewa maso gabashin Najeriya a jihar Borno.

Wannan hari dai an kai shi ne wajen rana, inda aka share awanni biyu ana kashe mutane kafin maharan su janye.

Bayan mutanen da aka kashe, rahotanni sun nuna cewa akwai shanu sama da dari uku da suma aka kashe sannan aka sace kusan dubu.

Bugu da kari, an samu bayanan cewa wannan hari an kaishi ne sa’o’i 24 biyo bayan harin da yan bindiga suka kaiwa masu ababen hawa akan titin Monguno.

Mazauna sun bayyana cewa akwai jama’a da yawa da suka samu raunuka.

Ya zuwa yanzu akwai mutane da yawa da ba’a san inda suke ba.

Wannan harin ya biyo bayan komawar shugaban hafsin sojan Najeriya Buratai Abuja domin bayyana wa Shugaban kasa irin nasarar da ake samu da yaki da Boko Haram, inda shugaban ya nuna murnar sa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *