Wani mai gabatar da labarai da harshen sipaniyanci ana zargin shi da neman wata mata da ba tashi ba, wadda ita ma tayi suna a lokacin da masu kallo suka hango wata mata babu kaya a jikinta, a lokacin da shi kuma yake aikin gabatar da labarai kai tsaye.

Mutumin mai suna Alfonso Merlos, mai shekaru 41 dake gabatar da shirin Estado de Alarma daga gidan shi saboda kullen annobar Korona, yana tsakiyar aiki ne kawai sai ga wata mata mara kaya a jikinta ta wuce ta bayan shi.

Mutane kuwa nan take suka gane ta, a matsayin Marta Lopez, wata taurauwan shirin Big Brother.

Mutumin bai ce komai ba na tsawon kwanaki sai da ya samu damar hallartar shirin Ana Rosa litinin dinnan, inda yayi neman gafara, kuma yace abunda yayi bai dace ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *