A yau 10 ga watan Yuni ne a ka yi karkare jana’izar binne bakar fatar nan George Floyd da wani farar fatar Dan Sanda Derek Chauvin ya hallaka ta hanyar danne dokin wuyansa da gwiwa har na tsawon mintin 8 da dakika 53.

HOTO: YANAR GIZO

An dai yi wannan jana’izar ne a cocin The Fountain of Praise church a garin Houston da nan ne marigayin yayi mafi yawancin rayuwarsa musamman ta kuruciya.

Dubban mutane ne suka taru tun jiya Talata garin Houston na jihar Texas ta Amurka don yin ban kwana da gawar Marigayin da a ke sa ran kisan sa zai iya zama sanadin kawo sauryi a yanayin ayyukan ‘yan sandan kasar.

A lokacin addu’o’in jana’izar, iyalan Marigayin suna kewaye da wasu iyalan da kwarzabar kisan gillar da ake wa bakaken fata ta shafa.

Kamar dangin wasu da suka mutu irin su Pamela Tuner da Botham Jean da Micheal Brown da kuma Eric Garner wanda ya yi kwatankwacin mutuwar George. Marigayi George ya bar mata daya da ‘yarsa ‘yar shekara 6 mai suna Gianna. 

‘Yar da a sakon ta’aziyyar dan takarar shugabancin Amurka a jam’iyyar Dimukurat Joe Biden ya ce, dole su Amurkawa su kalli cikin idonta su tambayi kawunansu me yasa ake wariyar launin fata a kasarsu?  

Wanda kafin mutuwarsa shima Eric ya dinga kukan cewa ya kasa numfashi, kamar yadda shima Floyd ya dinga wannan kukan neman dauki a lokacin da ya ke murkushe a kasan gwiwar Derek.

Kisan Floyd dai idan ba a manta ba ta ja kace nace a Amurka da ma duniya baki daya, inda zanga-zangata barke a kokarin rajin kare ‘yancin bakar fata da ‘yan sandan Amurka suka sha hallaka wa da sunan kame.

An haifi George a jihar North Carolina ta Amurka, inda daruruwan mutrane suka yi sahun kallon akwatin da gawarsa ke ciki don jama’a su yi masa ban kwana a ranar Asabar din da ta gabata.

Floyd ya gama makarantar Jack Yates High School a garin Houston din jihar Texas a shekarar 1992, makarantar da ya taimaka wa a kungiyar wasan kwallon kafarta da suka taba lashe gasar zakarun kwallon jihar. Sannan ya buga musu kwallon kwando.

Kafin Floyd ya koma inda ya gamu da ajalinsa da zama wato Minneapolis, ya taba kasance wa da wasu gungun mawakan zaurance ko ‘rap music’ a turance da a ke kiransu da sunan turanci ‘Screwed Up Clik’ ko ‘SUC’ a takaice.

An dai kori dan sanda Derek da ya kashe shi daga aiki tare da tuhumarsa gurfanar da aikata kisan gillar ganganci a mataki na biyu. 

Sannan an tuhumi sauran ‘yan sanda ukun da ke tare da shi da cewa sun taimaka wajen faruwar wannan lamari na kisan ba da gangan ba.

Har yanzu dai ana samun ‘yar zanga-zanga a nan da can a fadin duniya musamman Amurka game da neman samun ‘yancin bakar fata da kuma yi wa aikin ‘yan sandan kasar garambawul.

Kuna iya karanta yadda cikakken ragoton yadda a kashe George Floyd a bangaren  Rahotannin Musamman da ke kan yanar gizon nan tamu.

Ra’ayi 1

Your email address will not be published. Required fields are marked *