Mata ma’aikata sama da dari biyar ne a cikin su harda lauyoyi da masu gwagwarmaya, da ‘yan kasuwa da matan aure suka bazama akan tituna a Kalaba, Talatannan suna kira akan a gindaya dokoki da zasu taimaka wajen yiwa masu fyade dandaqa.

Masu bukatar hakan sun bayyana cewa wannan mataki zai taimaka wajen tsoratawa da hana masu aika irin wannan laifi.

Matan sanye da bakaken kaya sun rike alamu dake dauke da rubuce rubuce masu sakonni na dandaqa ga masu fyade.

Wasu daga cikin wadanda suka hallarta sun kunshi ‘yan siyasa kamar Ambasada Nkoyo Toyo, jakadiyar Najeriya a kasar Itopiya.

Masu zanga zanga sun bayyana cewa fyade ya zama ruwan dare, inda mata da yara da yawa suke samun kawunan su a cikin damuwa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *