Matasa da yawa ne suka tayar da zanga-zanga tare da toshi titin akan Titin Kankara a kusa da kauyen Yajntumaki dake karamar hukumar Danmusa, sakamakon rashin tsaro da ya addabi wajen.

Matasan dake wake waken yaki, sun cinna wuta akan titi inda suka ringa saka motoci da masu babura suna juyawa saboda gagara wuce hanya da suka yi.

Daruruwan masu ababen hawa ne suka yi watsi da wannan hanyar domin garin Katsina ko Gusau dake jihar Zamfara domin neman tsaro.

Wannan abu dai ya biyo bayan sace wani ma’aikacin kiwon lafiya Mansir Yusuf da diyar shi da aka yi a cikin al-ummar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *