MUHAMMADU BUHARI
SHUGABAN NAJERIYA

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya miƙa ta’aziyyarsa ga gwamnati da kuma al’ummar ƙasar Burundi bisa rasuwar Shugaban Ƙasar Pierre Nkurunziza.

Shugaba Buhari ya mika ta’aziyyar ce ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a Garba Shehu.

Ya ce marigayin mutum ne mai kishin ƙasa wanda ya jagoranci ƙasarsa a lokacin kunci, ta hanyar amfani da fasaharsa da hangen nesa.

Gwamnatin kasar Burundi ta ce Shugaba Pierre Nkurunziza ya rasu ne sakamakon bugun zuciya bayan ya shafe shekara 15 a kan mulki.

Shi ma Shugaban Nijar Issoufou Mahamadou ya miƙa tasa ta’aziyyar ga iyalan Nkurunziza da al’ummar Burundi a shafinsa na Twitter.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *