SHUGABAN BURUNDI

Gwamnatin Burundi ta ce shugaban Kasar Pierre Nkurunziza, ya mutu sakamakon bugun zuciya.

Nkurunziza ya mutu ne yana da shekaru 55 a duniya.

A ranar Asabar din da ta gabata ne aka garzaya da shugaban kasar Asibiti, domin kula da lafiyarsa.

A watan Augusta mai zuwa dama shugaban kasar zai sauka daga karagar mulki bayan kwashe shekaru 15 yana shugabantar kasar.

A shekarar 2015 ne matakin da Nkurunziza ya dauka na bayyana aniyar sake neman kujerar a karo na 3 ya jefa kasar cikin rudani.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *