Rundunar sojin Najeriya ta kashe ‘yan ƙungiyar Boko Haram da dama a Kwatara da ke kusa da Mandara na Jihar Borno.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hedikwatar tsaro ta fitar.

Ta ce dakarun rundunar Operation Lafiya Dole ne suka samu nasarar kashe ‘yan ta’addan da suka addabi jihar.

Ta ce sun kai samamen ne a ranar Litinin, inda suka yi nasarar kashe mayaƙan yayin da wasu suka tsere da raunuka.

Rundunar ta kara da cewa mayaƙan Boko Haram biyu sun rasa rayukansu a wani harin da aka kai musu a Darel Jamel da ke kan Titin Miyanti tare da ceto wata mace guda ɗaya a hannunsu.

Sojojin sun kuma kwato babur guda biyu da buhu cike da takalman roba da kuma kuɗi sama da naira dubu 29.
 
 

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *