Litinin dinnan ne majalisar wakilai ta kasa ta umarci babban ma’ajin kasa da babban bankin Najeriya akan su bada cikakken rahoto akan nera biliyan tamanin da uku da fadar shugaban kasa ta amince da shi domin yaki da annobar korona.

Shugaban kwamitin bin diddigin kudade, Wole Oke, shine ya bada wannan umarni a lokacin da yake jawabi a gaban gungun kwamitin shugaban kasa na yaki da Korona da Olusegun Adekunle ke jagoranta.

Oke yayi kira ga PTF akan ta mayar wa CBN ragowar kudaden da bata kashe ba.

Ya kuma kara da cewa kwamitin sa zata bincike yadda aka yi amfani da dala miliyan dari da ashirin da biyar wadda aka baiwa ma’aikatar lafiya ta kasa.

A halin yanzu dai, an fara sassauta dokar zauna a gida da jihohi ke yi, wannan ya kuma nuna cewa yaki da cutar Korona ya fara sanyi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *