MAIMALA BUNI
GWAMNAN YOBE

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya jajantawa al’umma musaman wadanda iftila’in rushewar gidaje ya shafa a fadin jihar.

Gwamna Buni ya kuma yi ta’aziya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon rushewar gidajen.

Gwamnan ya kuma yi rokon Allah Ya ba wadanda suka ji rauni sauki da waraka.

Gwamnan ya umurci hukumar bada agajin gaggawata jihar SEMA da ta lura da wayanda sukaji ciwo, su kuma dauki kiyasin barnar da aka samu domin taimaka musu.

Mai Girma Gwamna ya kuma umurci hukumar YOSEPA da ta tabbatar da yashe magudanan ruwa domin gudun faruwar haka a nan gaba.

A ranar Litinin din nan ne aka samu iftila’in rushewar gidajen a wasu garuruwa a jahar sakamakon ruwan sama hade da iska mai karfi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *