NASIR AHMAD EL-RUFAI
GWAMNAN KADUNA

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sassauta dokar taƙaita zirga-zirga na yaƙi da cutar Korona.

Gwamnan jihar Nasir Ahmad El-Rufai ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga ‘yan jihar a kafofin yada labarai.

Ya ce yanzu al’ummomin jihar za su riƙa hada hadarsu daga ƙarfe shida na safiyar kowacce rana zuwa takwas na dare.

Sannan ya bada umurnin bude masallatai tare da yin Sallar Juma’a kadai, yayin da Coci-coci za su rika budewa a ranakun Lahadi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *