AN GANO DAMIN ARZIKI BAYAN SHEKARA GOMA

Wani mutum dan asalin garin New Mexico dake Amurka ya yi gamo da gwala-gwalai da wasu kaya masu matukar daraja sama da dala miliyan daya.

Shekara goma da suka gabata ne Forrest Fenn ya samue magoya baya a lokacin da ya ce ya boye arziki a cikin duwatsun Rockey. Wannan ya harzuka mutane sama da dubu goma suka bazama neman wannan arziki, kuma aka gagara samowa sai yanzu.

Fenn ya nuna wa jaridar Santa Fe New Mexian Lahadin nan cewa wani mutum, wanda ya nemi a sakaye sunanshi, ya samo arzikin kwanakin da suka gabata. Mutumin da ya samo, ya aika wa Fenn hoton arzikin domin tabbatar wa ya samo shi.

Abunda ya sa Fenn ya saka wannan gasa shi ne, a shekara ta 1989, an gano yana da cutar daji kuma ba a yi tunanin zai rayuwa ba, amma kuma ga shi ya warke. To shikennan ya yi alwashin bai wa mutane abun yi mai kayatarwa, kamar shiga cikin daji da hawa duwatsu domin neman arziki. An yi lissafin a kalla mutane dubu dari uku da hamsin ne suka je neman arzikin basu samu ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *