Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da shugaban rundunar sojin ƙasa ta Najeriya, Laftanal Janar Yusuf Tukur Buratai a fadar Shugaban Ƙasa dake.

Sanarwar da fadar shugaban ta wallafa ta ce Buratai ya gana da shugaba Buhari ne domin masa bayani kan nasarori da rundunar soji ke samu a yaƙi da ƙungiyar Boko Haram.

Tun bayan komawar Buratai yankin arewa maso gabas domin jagorantar yaƙi da ‘yan ta’addan Boko Haram, rundunar sojin ke ci gaba da samun nasarori.

Sanarwar ta ƙara da cewa mayaƙan ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP 1,400 aka kashe a yankin sannan aka kama ‘yan leƙen asirin kungiyar 166.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *